Likafa ta ci gaba: Shugaban majalisar dinkin Duniya ya nada Amaechi babban mukami

Likafa ta ci gaba: Shugaban majalisar dinkin Duniya ya nada Amaechi babban mukami

Majalisar dinkin Duniya ta sanar da wani muhimmin nadi da ta yi ma tsohon gwamnan jihar Ribas, kuma ministan sufurin Najeriya, Chibuike Rotimi Amaechi, wanda ta nada shi mamba a kwamitin gudanarwa na gidauniyar kiyaye haddura akan tituna na Duniya.

Jaridar Africanjournalist.info ce ta bayyana haka a shafinta, inda tace majalisar ta sanar da nadin Amaechi ne a Geneva, kasar Switzerland, wanda a yanzu haka ministan yana can kasar, inda yake wakiltar Najeriya a taron gidauniyar dake gudana.

KU KARANTA: Babban sufetan Yansanda ya bayyana abubuwa 10 da suka bankado a yayin bincikar Lawal Daura

Likafa ta ci gaba: Shugaban majalisar dinkin Duniya ya nada Amaechi babban mukami
Amaechi a Geneva

Majalisar ta nada Amaechi ne domin ya kirkiro hanyoyin rage aukuwar haddura, rage adadin mutanen da hatsari ke rutsawa dasu tare da tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin mutane akan hayoyin Duniya gaba daya.

Legit.ng ta ruwaito haidimin Ministan akan kafafen watsa laabru, Israel Ibeleme yace tattaunarwa da ake gudanarwa a yanzu haka a Geneva, da kuma shawarwarin da za’a yanke a can, zasu taimaka matuka wajen ganin gidauniyar ta amfani al’ummar Duniya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel