Hauka tuburan! Yadda wani taɓabbe ya lakaɗa ma Likita dukan tsiya a Asibitin mahaukta dake Ondo
Hankula sun tashi, an samu hatsaniya a babban Asibitin mahaukata dake garin Akure na jihar Ondo a ranar Alhamis, 9 ga watan Agusta, inda wani mara lafiya, Folorunsho Olawale ya lakada ma ma’aikatan asibitin dan banzana duka, inji rahoton jaridar Sahara.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin wadanda suka ci dukan har da babban likitan Asibitin kuma shugaban Asibitin, Dakta Akinwumi Akinloye, wanda tsabar jibga har sai da ya suma ya fita hayyacinsa.
KU KARANTA: Babban sufetan Yansanda ye nemi izinin yin binciken kwakwaf akan Lawal Daura
Baya ga shugaban Asibitin, wasu ma’aikatan jinya guda hudu da wani Likita Dakta Sunday Sajo sun ji ajikinsu a lokacin da ya haukar Lawal ta motsa, haka zalika Lawal ya lalata kayan asibitin da dama.
Shi dai Lawal ya samu kansa a wannan Asibiti ne bayan Yansanda sun kai don a duba lafiyarsa, a cewarsu shi da kansa ya kai kansa Ofishin Yansanda dake Akure kuma ya bayyana musu cewa yana da hannu cikin kisan Khadijat Oluboyo, diyar tsohon mataimakin gwamnan jihar Ondo, Lasisi Oluboyo.
Da wannan dalilin ne Yansandan suka dacewar su mika shi Asibiti don a duba lafiyar kwakwalwarsa, sai dai a ranar Alhamis jikinsa ya tashi, inda nan da nan wasu ma’aikatan jinya suka yi kokarin yi masa allura, daga nan ne fay a dinga casa duk wanda ya kama, tare da barnata kayan aiki.
Sai dai ma’aikatan asibitin sun yi bore, sakamakon umarnin komawa bakin aiki da babban sakataren hukumar kiwon lafiya na jihar, Adeniran Ikumola ya basu, duk da ganin halin da ake ciki a lokacin.
“Mun yi zanga zanga, kuma ba zamu koma bakin aikinmu ba tunda babu tsaro, kuma babban sakatare bai nuna damuwarsu da halin da muke ciki ba.” Inji ta.
A nasu jawabin, rundunar Yansandan jihar ta bakin Kaakakinta, Femi Joseph ta tabbatar da faruwar lamarin, inda tace tuni suka tura da jami’ansu zuwa Asibitin don lura da Lawal.”
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng