Hukumar Kwastam ta kama mutane 8 dake fataucin Kodin da miyagun kwayoyi
Jami’an hukumar kwastam sun kama wata mota kirar MAN Diesel makare kwalaben kayan shaye shaye da suka hada da Kodin da sauran miyagun kwayoyin a tsakanin 25 na Yuli zuwa 7 ga watan Agusta, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
Shugaban sashi na daya na hukumar, Mohammed Uba ne ya sanar da haka a ranar Alhamis, inda yace sun kama kayan shaye shayen ne kusa da babbar kasuwar Alaba dake jihar Legas, inda yace akwai kwalaben kodin guda dubu dari biyu da saba’in da hudu da dari takwas (274,800).
KU KARANTA: Hawainiyarka ta kiyayi ramar Baba Buhari – Iyaye Mata ga Obasanjo
Majiyar Legit.ng ta ruwaito akwai katan 95 na kwayar Chaka, an kintata darajar kayan maye akan kudi naira biliyan daya. Kwantrokla Uba yace baya ga wadannan, jami’ansu sun kama wasu katan 49 na kwayar Tramadol da kuma buhuna 21 na Pangolin a wani shago dake kasuwar tejusho, wanda yace sun kai darajar naira miliyan 253.
Uba yace: “Mun sake kama wata mota kirar Ford a garin Olorunda na jihar Ogun, dauke da buhuna 39 da kunshi 1,220 na tabar wiwi, da nauyinsu ya kai kilo 1,610, wanda aka rufesu da Tumatir da kayan lambu, kuma zamu mikasu ga hukumar kula da tsaftar abinci.”
Daga karshe Malam Uba yace sun kama mutane takwas dake da hannu cikin safarar miyagun kwayoyin, kuma zasu mika su gaban Kotu da zarar sun kammala bincike.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng