Kungiyar kasashen Turai, EU, ta bayyana damuwa kan mamayar da Hukumar DSS ta yiwa Majalisar Tarayya

Kungiyar kasashen Turai, EU, ta bayyana damuwa kan mamayar da Hukumar DSS ta yiwa Majalisar Tarayya

Da sanadin shafin jaridar Premium Times mun samu rahoton cewa, kungiyar kasashen turai watau EU (European Union), ta bayyana ra'ayin ta a ranar Alhamis ta yau dangane da mamayar da hukumar DSS ta kai farfajiyar majalisar dokoki ta tarayya a ranar Talatar da ta gabata.

Ko shakka ba bu a ranar 7 ga watan Agustan da ta gabata ne hukumar DSS ta Najeriya ta mamaye tare da yiwa farfajiyar majalisar dokoki ta tarayya kawanya gami da hana 'yan majalisar samun damar shiga domin gudanar da zaman su.

A sanadiyar wannan lamari ne ya sanya kungiyar ta kasashen turai ta bayyana damuwar ta dangane da aukuwar wannan lamari da cewar zagon kasa ne ga dimokuradiyyar kasar nan.

Kungiyar kasashen Turai, EU, ta bayyana damuwa kan mamayar da Hukumar DSS ta yiwa Majalisar Tarayya
Kungiyar kasashen Turai, EU, ta bayyana damuwa kan mamayar da Hukumar DSS ta yiwa Majalisar Tarayya

A yayin da kungiyar ta dukufa wajen kare martabar dimokuradiyyar kasar nan ta Najeriya, ta gargadi hukumomin tsaro akan amfani da su wajen cimma manufofin siyasa kasancewar majalisar tarayya wani ginshiki ne ga dimokuradiyyar kowace kasa.

Kungiyar ta kuma yabawa gwamnatin tarayyar Najeriya dangane da matakin gaggawa da ta dauka kan wani lamari mai tattare da abun kunya da takaici sakamakon zagon kasa da zai sanadi ga dimokuradiyyar kasar nan.

KARANTA KUMA: Zaben 2019: Ba bu wani 'Dan Takara na PDP da zai iya nasara akan Buhari - Fadar Shugaban 'Kasa

Legit.ng ta fahimci cewa, mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya gaggawar tsige shugaban hukumar ta DSS, Lawal Daura, sa'o'i kadan bayan cecekuce da lamarin ya janyo a fadin kasar nan.

Mukaddashin shugaban kasar ya bayyana cewa, ya yanke wannan hukunci ne sakamakon gaban kansa da shugaban hukumar ta DSS ya yi da kuma tabbatar da kiyayen tsare-tsare da doka da gwamnatin shugaba Buhari ta dukufa a kai.

Rahotanni sun bayyana cewa, mukaddashin shugaban kasar ya samu yabo a fadin Najeriya har daga bangaren abokanan adawa, da kuma wasu 'yan majalisar da a baya suka yi suka a gare sa dangane da rikon sakainar kashi da ya yiwa lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel