Ta tabbata: Tsohon hadimin shugaban DSS ya fallasa yadda yake karbar cin hanci da rashawa

Ta tabbata: Tsohon hadimin shugaban DSS ya fallasa yadda yake karbar cin hanci da rashawa

Malam Abdulwahab Abdulrahman, tsohon babban jami’I a hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, kuma tsohon hadimin tsohon shugaban hukumar Lawal Daura, haka zalika tsohon abokin aikinsa ya fallasa yadda Lawal ya ci amanan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A ranar Talata, 7 ga watan Agusta ne mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya sallami Lawal Daura daga aiki tare da tsigeshi daga mukamin shugaban hukumar DSS, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Kafa da kafa: Shekarau ya yi takakkiya zuwa gidan Fani Kayode, maci mutuncin Arewa

Abdulrahman ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da jaridar Premium Times, inda yace Buhari bai san Lawal Daura ba sai a shekarar 2015 bayan marigayi Sanata Mustapa Bukar ya hada shi da Buharin, amma duk da haka Buhari ya amince masa, sakamakon ya kama dan uwan Buhari Mamman Daura.

Ta tabbata: Tsohon hadimin shugaban DSS ya fallasa yadda yake karbar cin hanci da rashawa
Lawal

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Abdulrahman na cewa a dalilin tsagwaran halin cin hanci da rashawa na Lawal Daura ya sanya shi yin murabus daga aikinsa, tare da raba gari da tsohon Maigidan nasa.

Abdulrahman yace yana daga cikin masu kula da tsaro tare da Lawal Daura a yayin yakin neman zaben shugaban kasa Buhari, haka kuma yana cikin kwamitin amsan mulki tare da Lawal Daura da Buhari ya kafa bayan ya lash zabe.

Sai dai yace a duk ayyukan nan da suka yi, ya fahimci Lawal Daura kudi kawai yake nema, “Wata rana ce min yayi mu nemi naira biliyan daya don aikin tsaro a yayin yakin neman zabe, a ina Buhari zai samu kudin nan?” Inji shi.

Abdulrahman ya tabbatar ma majiyarmu cewa Lawal Daura bai cancanci zaman shugaban DSS ba, saboda bai taba aiki a babban ofishinsu dake Abuja ba, kuma baya fita aiki a waje, amma hawansa keda wuya sai ya dinga karbar kudi har ma daga makiyan Buhari.

“A wasu lokuttan babu abinda muke yi a Ofis face kirga kudi, tun daga safe har karfe biyun dare, har ta kai ga sai dai mu kira yan Canji su zo su samemu a Ofis don canjin kudi, bugu da kari Lawal na samo ma Saraki bayanan sirri daga Gwamnati.” Inji shi.

Bugu da kari Abdulrahman yace dalilin da yasa Lawal Daura baya shiri da Magu, har ma ya shirya masa makarkashiya a majalisar dattawa shine Magu ya hana shi wasu muhimman bayanai na wasu manyan mutane da ake bincika don tsoron kada ya fallasa musu bayanan.

Daga karshe Abdulrahman yace dama Lawal ya saba sata, inda yace ya sace motoci 20 da Tinubu ya saya ma DSS a zamanin yana gwamna, lokacin da Lawal ke shugaban DSS a jihar, kuma an taba kama shi yana satar man Dizil a kwalejin DSS dake Kaduna.

Sai dai dukkanin kokarin da majiyarmu ta yi don tabbatar da wadannan bayanai abin yaci tura, sakamakon wanda ake maganan akansa, Lawal Daura yana hannun gwamnati a daure.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng