Ga lada ga la’ada: Wani Dan kasar China ya auri Bahaushiya bayan ya Musulunta a Filato (Hotuna)

Ga lada ga la’ada: Wani Dan kasar China ya auri Bahaushiya bayan ya Musulunta a Filato (Hotuna)

Rayuwa kenan, masu iya magan sun ce idan rai toh da rabo, anan wani matashi dan kasar China ne ya taso tun daga uwa Duniya, inda har sai a garin Wase na jihar Filato ya karbi Musulunci.

Legit.ng ta ruwaito wani karin abin ban sha’awa game da wannan dan kasar China shine, dayake dama matar mutum kabarinsa, kuma mutum ba zai aura wata ba illa matarsa, sai matashin ya samu wata tsaleliyar budurwa, ya nuna sha’awarsa.

KU KARANTA: An kashe mutane 3 a rikici tsakanin makiyaya da yan kasuwar awaki a Adamawa

Ga lada ga la’ada: Wani Dan kasar China ya auri Bahaushiya bayan ya Musulunta a Filato (Hotuna)
Miji da Mata

Rahotanni sun tabbatar da bayan musuluntarsa, Matashin ya sauya sunansa zuwa Samir, inda bayan da Samir ya fara neman wannan budurwa, kuma suka fahimci juna, sai ya nemi a bashi aurenta, haka kuwa aka yi, inda aka aura masa sahibar tasa.

Shi dai garin Wase ba bako bane ga Chanisawa, inda sun dade shekara da shekaru suna zuwa garin domin aikin hakar ma’adanan kasa, tun bayan da suka gano tsabar albarkar dake jibge cikin kasar Wase.

Ga lada ga la’ada: Wani Dan kasar China ya auri Bahaushiya bayan ya Musulunta a Filato (Hotuna)
Bachanishen

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng