'Yan bindiga sun kashe Hausawa 'yan canjin kudi 4 a garin Fatakwal
Labarin da muke samu daga majiyar mu ta BBC Hausa na nuni ne da cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga dadi ne sun harbe wasu Hausawa masu sana'ar canjin kudaden kasar waje a garin Fatakwal, babban birnin jihar Ribas dake a kudu maso kudancin Najeriya.
Kamar dai yadda muka samu wadanda aka kashen din sun hada da Ahmad A. Tukur da Yusuf Zaki da Muhammad Rabi'u da kuma Abubakar Tugga.
KU KARANTA: Abu 5 da ya kamata ku sani game da Lawal Daura
Legit.ng ta samu cewa 'yan bindigar dai sun kashe mutanen ne gidansu da ke a karamar hukumar Obiako da ke Fatakwal, babban birnin jihar Rivers.
Haka ma kuma rahotannin farko-farkon da muka samu na nuna cewa ana zargin turo 'yan bindigar akayi domin kisan ya biyo bayan wata takaddamar rufe wata kasuwa ne tsakanin mamatan, da wasu jam'ian gwamnatin Ribas, domin maharan ba su dauki komai ba bayan kisan da suka kaddamar.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng