Mu ma 'yan kallo ne kamar kowa - Jam'iyyar APC tayi tsokaci game da samamen da aka kai majalisa

Mu ma 'yan kallo ne kamar kowa - Jam'iyyar APC tayi tsokaci game da samamen da aka kai majalisa

Jami'iyya mai mulki a Najeriya ta All Progressive Party (APC) ta karyata jita-jitan da ke ta yawo na cewa wai tana da hannu a cikin takaddamar zagaye majalisa da jami'an tsaron farin kaya suka yi da safiyar yau.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da jami'in hulda da jama'a na jam'iyyar na rikon kwarya mai suna Yekini Nabena a fitar dauke da sa hannun sa inda yace suma 'yan kallo ne kamar sauran yan Najeriya.

Mu ma 'yan kallo ne kamar kowa - Jam'iyyar APC tayi tsokaci game da samamen da aka kai majalisa

Mu ma 'yan kallo ne kamar kowa - Jam'iyyar APC tayi tsokaci game da samamen da aka kai majalisa

KU KARANTA: Osinbajo ya fadi dalilin da yasa ya tsige Lawal Daura

Legit.ng ta samu cewa sanarwar ta kara da cewa ya kamata 'yan Najeriya su cire su daga cikin wannan rigimar domin kuwa harka ce da ta shafi jami'an tsaro da kuma yan majalisa.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya tsige shugaban hukumar tsaro ta sirri, wato DSS, Malam Lawal Daura daga mukaminsa biyo bayan farmakin da jami’an hukumar suka kai majalisar dokokin Najeriya da safiyar ranar Talata 7 ga watan Agusta.

Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa Osinbajo, Laolu Akande ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 7 ga watan Agusta.

Haka zalika hadimin shugaban kasa Buhari akan harkokin sadarwar zamani, Bashir Ahmad ya tabbatar da fatattakar Lawal Daura daga aiki. Bugu da kari, Farfesa Osinbajo ya umarci Lawal Daura ya mika ragamar tafiyar da hukumar ga jami’I mafi girma a hukumar, har sai baba ta ji.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel