Sabbin takunkumai masu kuntatawa kan kasar Shi'a ta Iran daga Amurka
- Amurka ta kara tabbatar da hukuncin ta akan Iran a ranar talata
- 'Yan kasar Iran har sun fara ganin illolin hukuncin
- Trump ya tashi yarjejeniyar su da Iran akan shirin din nukiliya
Dawo da tsauraran hukunce hukunce da aka janye, yarjejeniyar hadin guiwa da shugaban kasa Donald Trump yayi watsi da ita.
Matakai guda biyu na farko sun fara aiki ne a karfe 12:01am inda aka saita su akan hanyar da Iran take samun kudaden US da makullan ma'aikatu, hadi da motoci.
Baya da hakan, kudin Iran ya rage daraja ta kusan rabin shi tunda shugaba Trump ya sanar da janyewar su daga yarjejeniyar 2015 ta nukiliya.
Janyewar bangare dayan ta yarjejeniyar hadin guiwa ta yuwu duk da sauran masu yarjejeniyar - Birtaniya, Chana, Faransa, Jamani, Rasha da EU - sun roki Trump da kada yayi watsi da hanyar toshewa Iran din damar samun makamin nukiliya.
Shugaban kungiyar diflomasiyyar turai, Federica Mogherini tace Birtaniya, Faransa da Jamus suna matukar dana sanin yunkurin na Washington.
Da yawa daga cikin masana'antun turai na barin Iran saboda tsoron hukuncin US, kuma Trump ya ja kunne ga mutane da masana'antu da zasu cigaba da kasuwanci da Iran.
Ba akan ta tsaya ba, tashin hankali ya fara a Iran bayan kwanaki kadan da janye yarjejeniyar, inda mutane ke ta zanga zanga da yajin aiki akan rashin ruwa, karuwar kudaden kayayyaki da kuma tashin hankali siyasar kasar.
DUBA WANNAN: Asarar jama'a zuwa ga talauci a Najeriya
Kashi na biyu a hukuncin US zai zo ne a 5 ga watan Nuwamba inda US zata toshe kasuwancin mai da Iran, wanda zai jawo babbar illa ga kasar. Amma kasashe irin su Chana, India da Turkiyya sun nuna rashin amincewar su da yanke hulda da kasar Iran din.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng