Obasanjo ne ya kafa tushen mummunan jagoranci a Najeriya - Osoba

Obasanjo ne ya kafa tushen mummunan jagoranci a Najeriya - Osoba

Tsohon gwamnan jihar Ogun, Cif Olusegun Osogba, ya kaca-kaca da tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Osabanjo, dangane da rawar da ya taka gami da ruwa da tsaki wajen kafa mummunan jagoranci da mulkin kama karya a kasar nan.

Tsohon gwamnan kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, ya na tuhumar tsohon shugaban kasa Obasanjo wajen kafa duk wani tushe na mummunan jagoranci a kasar nan.

Osogbo yake cewa, tsohon shugaban kasar ya yi babakere wajen kulla tuggu da mugudi a tsakanin gwamnonin da aka zaba karkashin jam'iyyar AD (Alliance for Democracy) a shekarar 1999, wanda wannan shine tushen gurbata duk wani jagoranci a Najeriya.

Obasanjo ne ya kafa tushen mummunan jagoranci a Najeriya - Osoba
Obasanjo ne ya kafa tushen mummunan jagoranci a Najeriya - Osoba

Tsohon dan jaridar da ya sauya zuwa harkokin siyasa ya bayyana cewa, zaben gwamnoni a shekarar 1999 da aka gudanar karkashin mulkin Obasanjo, shine mugun irin da ya assasa duk wani gurbataccen shugabanci a kasar nan.

KARANTA KUMA: Yadda Gwamnatin Tarayya ke amfani da Kuɗaɗen da Abacha ya sace

Legit.ng ta fahimci cewa, Osoba ya bayyana hakan ne a ranar Litinin din da ta gabata cikin birnin Legas yayin halartar bikin cikar shekaru 70 na mamallakin kamfanin mujallar Newswatch, Mista Ray Ekpu.

Sauran wadanda suka halarci wannna taro sun hadar da; tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom; Obong Victor Attah, Sam Amuka-Pemu mai kamfanin jaridar Vanguard, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin kasa; Farfesa Pat Utomi da sauran jiga-jigai a faggen aikin jarida.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng