Tattalin arziki: Babban bankin Duniya ya gargadi Gwamnatin Buhari
Babban bankin Duniya ta gargadi Gwamnatin Najeriya ta bi sannu a hankali da karbo bashi inda aka nemi a maida hankali wajen jawo hannun jari cikin kasar domin gudun shiga cikin matsala.
Bashin da ke kan wasu kasashen Afrikan irin Najeriya ya fara yawa. Sai dai manyan Jami’an Gwamnatin Kasar sun hakikance cewa tattalin kasar bai cikin hadari idan aka duba karfin tattalin Najeriya da kuma nauyin bashin ta.
Najeriya dai ta ci bashin kusan Tiriliyan 6 a cikin shekaru 3 domin cike rarar kasafin kudin kasar a mulkin Shugaba Buhari kamar yadda Jaridar Business Day ta bayyana. Dalilin haka ne babban bankin Duniya ta ke ganin a sake tunani.
KU KATANTA: Jam’iyyar PDP ta tonawa Gwamnatin Shugaba Buhari asiri
Babban Jami’in na bankin Duniya na Yankin Afrika Hafez Ghanem ya bayyana cewa a maimakon Najeriya tayi ta cin dan-karen bashi, gara ta jawo ‘Yan kasuwa cikin kasar su gina abubuwan more rayuwa ba tare da an kakabawa mata nauyi ba.
Hafez Ghanem ya kuma nemi Gwamnatin Najeriya ta maida hankali wajen samun kudi shiga ta tatsar haraji da sauran su. Jami’in na babban Bankin Duniya yace dole tattalin arzikin Najeriya ya bunkasa idan har ana neman ayi yaki da talauci a Kasar.
Daga cikin rarar kusan Tiriliyan 2 da ke cikin kasafin Najeriya na bana, ana sa rai za a ci bashin Tiriliyan 1.63 ne wanda akalla Biliyan 800 za su fito daga kasashen waje. Sabon Mataimakin Shugaban babban bankin Duniyar dai yace akwai gyara.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng