Babban Sanatan Jam’iyyar PDP Godswill Akpabio ya bar matsayin sa

Babban Sanatan Jam’iyyar PDP Godswill Akpabio ya bar matsayin sa

Labari ya zo mana ba da dadewa ba cewa Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Godswill Akpabio ya aika takarda inda ya tabbatar da cewa ya ajiye mukamin na sa.

Babban Sanatan Jam’iyyar PDP Godswill Akpabio ya bar matsayin sa
Sanata Akpabio na Jam’iyyar PDP ya ajiye aikin sa

Sanatan na Yankin Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma ya aikawa Mataimakin sa Sanata Emmanuel Bwacha wata doguwar wasika a Ranar Asabar inda yace ya bar mukamin na sa na Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa.

Godswill Akpabio bai bayyanawa Mataimakin na sa dalilin daukar wannan mataki ba, sai dai ya godewa ‘Yan uwan sa na Jam’iyyar PDP da su ka ba shi daman zama shugaban su a Majalisar Dattawan Kasar na tsawon fiye da shekara 3.

KU KARANTA: DSS sun zagaye harabar Majalisar Tarayyar Najeriya

Babban Sanatan Jam’iyyar PDP Godswill Akpabio ya bar matsayin sa
Wasikar Shugaban Sanatocin Jam’iyyar PDP Godswill Akpabio

‘Dan Majalisar ya kuma godewa Jam’iyyar PDP da goyon bayan da ta ba shi na rike wannan kujera. Sanatan na Akwa Ibom da yanzu ake rade-radin cewa ya fice daga PDP ya koma APC bai tabbatar da hakan ba a cikin wasikar ta sa.

Kwanaki ne Tsohon Gwamnan na Akwa Ibom yana cikin manya a Majalisa ya gana da Shugaba Buhari a Landan. Bayan dawowar sa kuma ya zauna da Jigon Jam’iyyar APC watau Bola Tinubu a Abuja inda ake tunani zai koma Jam’iyyar APC.

Dama kun san cewa wani Sanata ya bayyana cewa da zarar an dawo hutun da Majalisa ta tafi za a tsige Bukola Saraki wanda ya koma PDP, ba mamaki a maye gurbin na sa da Sanata Godswill Akpabio wanda shi kuma ke neman shigowa APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng