Akwai mugun yaudara a lamarin Shugaba Buhari – Inji Jam’iyyar PDP
Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya yaudari jama’ar kasar nan da sunan yaki da cin hanci da rashawa da kuma aiki da gaskiya wajen hawa mulki a zaben 2015.
Jam’iyyar PDP tace Gwamnatin Shugaba Buhari ba ta cika wadannan alkawari da ta dauka ba illa yaudarar mutanen gida da waje da ta rika yi. PDP a wani jawabi da ta fitar kwanan nan tace ba abin da Gwamnatin nan ta sa a gaba sai karya.
Kamar yadda labari ya zo mana, PDP ta zargi Gwamnatin APC da aikata manyan laifuka 14 inda aka wawaure kudin al’umma ba tare da Shugaban kasa Buhari yayi komai ba. Daga cikin wadannan laifi akwai zargin da ke kan Ministar kudi.
KU KARANTA: Ana zagin NNPC da kitsa tsige Bukola Saraki daga matsayin sa
PDP ta zargi Kamfanin NNPC da yin awon gaba da sama da Tiriliyan 1.4 da sunan tallafin man fetur. Bayan nan kuma PDP na zarhin Gwamnatin Buhari da sace Biliyan 18 daga cikin kudin da aka ware domin ‘Yan gudun Hijiran Boko Haram.
Har wa yau PDP na zargin wannan Gwamnati da lashe wasu Tiriliyan 1.1 wajen harkar shigo da man fetur cikin Najeriya. PDP tace Buhari yana karyar yaki da sata ne kurum domin cin ma bukatun sa amma a zahiri satar dukiyar kasar ake yi.
Dazu kun ji labari cewa Sanatan Kaduna ta Arewa Suleiman Othman Hunkuyi ya nemi Jama’a su tika APC da kasa a zabe mai zuwa saboda mawuyacin halin da su ka jefa al’ummar Kasar nan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng