2019: 'In sun kawo kudinsu ku amsa, amma ku zabi na gari' - Dan takarar shugaban kasa a PDP
- Makarfi ya bawa al'umma shawara akan yan takara
- Yayi wannan furuci ne a Lokoja yayin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki na PDP
- Makarfi yace indai har yabar jam'iyar PDP to ya gama siyasa ne baki daya
Tsohon gwamnan jahar Kaduna Ahmed Makarfi sannan kuma cikakken dan jam'iyar PDP ya shawarci al'umma da su karbi duk wata kyauta da yan takara zasu basu sannan su zabi mai nagarta da gaskiya.
Kamar dai shagube yake kan sabbin masu shigowa jam'iyyar don neman takara ko sayen mukamai daga APC
Makarfi yayi wannan furuci ne a Lokoja inda ya gana da masu ruwa da tsaki da shuwagabanni na jam'iyar PDP a jahar Kogi inda yake neman goyan bayansu akan takarar shugabancin kasa da yake nema.
DUBA WANNAN: Najeriya na asarar jama'arta ga talauci
Sanata Makarfi ya taimaka wa Shugaban kasa Obasanjo a 2007 sannan ya zama mataimakin Shugaban kasa Goodluck Jonathan amma wasu dalilai ya sakashi sauka inda daga baya yake rike da jam'iyar.
Ya kara da cewa inda har yabar jam'iyar PDP to ya gama siyasa ne baki daya.
Yayin da yake bawa manema labarai amsoshin tambayoyin su a sakateriyar PDP dake Minna a ranar Asabar yace "Koda bai samu nasarar za ma dan takarar shugaban kasar ba to bazaibar PDP ba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng