An huro ma Tambuwal wuta sai ya yi murabus daga kujerarsa ta Gwamna

An huro ma Tambuwal wuta sai ya yi murabus daga kujerarsa ta Gwamna

Wasu kungiyoyin masu kishin jihar Sakkwato sun bukaci gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da ya yi murabus daga kiujerar gwamnan daya shantake akai, tunda dai ya sauya sheka daga jam’iyyar da ta kai shi ga zama gwamna, APC zuw PDP.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kungiyar ta bayyana haka ne ta bakin shugabanta, Alhaji Abubakar Abdullahi a ranar Lahadi, 5 ga watan Agusta, inda yace sauyin sheka da Tambuwal ya yi tamkar cin amanar jama’an sakkwato ne.

KU KARANTA:Masu garkuwa sun saki Sheikh Al-Garkawy bayan karbar miliyoyin kudin fansa

Kungiyar ta ce Tambuwal ya zama gwamna a inuwar APC ne ba wai don ya fi kowa iyawa bane, amma sakamakon halin da jam’iyyar PDP take tafiyar da kasar, da kuma samun goyon bayan shugaba Buhari da Sanatan Wammako da ya yi.

An huro ma Tambuwal wuta sai ya yi murabus daga kujerarsa ta Gwamna
Gwamna

Haka zalika kungiyar ta yi kira ga hukumomin yaki da rashawa dasu binciki zargin da yan majalisun jihar suka yin a cewa Tambuwal ya basu miliyoyin nairori don su bi shi zuwa PDP, haka zalika sun bukaci Tambuwal ya yi ma Sakkwatawa bayani game da nair miliyan 5 da ya kashe ma kowanne karamar hukumar da ta aiko da wakilanta fadar gwamnati a ranar da ya fice daga APC zuwa PDP.

Bugu da kari Abubakar ya yi alwashin zasu wayar da kan jama’a game da hanyoyin yin kiranye ga duk dan majalisar da ya sauya sheka daga APC zuwa PDP, sa’annan ya bayyana maganganun da Tambuwal yayi game da gwamnatin tarayya a matsayin karairayi.

Abdullahi yace gwamnati ta kafa rundunar Soji ta takwas a jihar Sakkwato, gwamnati ta kashe naira biliyan 8.7 akan harkar noma a jihar Sakkwato, haka zalika gwamnati ta baiwa jihar Sakkwato naira biliyan 18.3 na kudin Paris, da kuma tallafin biyan albashi na naira biliyan 10.9, da wannan ne yayi kira ga Tambuwal da ya bayyana ma Sakkwatawa yadda ya kashe kudaden.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng