Akwai kallo: Gwamnan Gombe Dankwambo zai yi takarar Shugaban kasa a 2019

Akwai kallo: Gwamnan Gombe Dankwambo zai yi takarar Shugaban kasa a 2019

Mun samu labari ba da dadewa ba cewa Gwamnan Jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo ya shirya fitowa takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar adawa PDP a zabe mai zuwa na 2019.

Akwai kallo: Gwamnan Gombe Dankwambo zai yi takarar Shugaban kasa a 2019
Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo zai yi takarar Shugaban kasa a zaben 2019

Hakan na zuwa ne bayan wani ‘Dan takara a PDP watau tsohon Shugaban Jam’iyyar kuma tsohon Gwamnan Kaduna Ahmad Makarfi ya kai wa tsohon Shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida ziyara domin a sa masa hannu.

Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo na Gombe ya tabbatar da cewa zai tsaya takarar Shugaban kasa a zaben 2019. Gwamnan ya bayyana wannan ne lokacin da ya gana da wasu manyanJam'iyyar PDP na Arewa a jiya Ranar Asabar.

KU KARANTA: Atiku yayi wa Jama’a wani babban alkawari idan har ya zama Shugaban kasa

Ibrahim Hassan Dankwambo yayi wani zama da Jagorarin PDP na Yankin Arewa maso Gabas inda daga nan ne Gwamnan ya fito. Dankwambo yace Jama’a da dama sun huro masa wuta cewa ya fito takarar kujerar Shugaban kasa.

Gwamnan na Jihar Gombe yace ba zai dauki mataki ba tare da ganawa da ‘Ya ‘yan Jam’iyyar sa ba, don haka ne ya tara kusoshoshin PDP na Arewa maso Gabashin kasar ya sanar da su matakin da ya dauka inda ya nemi goyon bayan su.

Akwai dai tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da ya fito daga wannan Yanki duk kuma a Jam'iyyar PDP. Sai dai tsohon Shugaban kasar nan watau Cif Olusegun Obasanjo ya nuna cewa sam ba zai marawa Atiku baya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng