Hukumar Sojin Sama ta tarwatsa wata Maboyar 'Yan Boko Haram a Jihar Borno

Hukumar Sojin Sama ta tarwatsa wata Maboyar 'Yan Boko Haram a Jihar Borno

Mun samu cewa, a ranar Juma'ar da ta gabata ne hukumar sojin sama ta Najeriya, ta samu nasarar kai wani hari na tarwatsa wata maboyar 'yan Boko Haram dake garin Daban Masara a jihar Borno.

Hukumar ta cimma wannan nasara ne sakamakon wani bincike na leken asiri da ta gudanar, wanda ya tabbatar da cewa akwai tsirari na ragowar 'yan Boko Haram da suke labe a tsuburburan dake gabar tafkin Chadi.

Binciken na leken asiri da hukuma sojin ta gudanar ya tabbatar da cewa, 'yan ta'addan na labe ne cikin wasu gidaje daka Kudancin gabar tafkin Chadi a garin na Daban Masara.

Rahotanni kamar yadda hukumar ta bayyana a shafin ta na sada zumunta sun bayyana cewa, an yi amfani da wani jirgin yaki kirar Alpha Jet na hukumar wajen tarwatsa wasu gidaje biyu dake tsuburin na tafkin Chadi.

KARANTA KUMA: Ba zan taba goyon bayan Atiku a matsayin shugaban 'Kasa ba - Obasanjo

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, fitaccen lauya mai kare hakkin dan Adam Femi Falana, ya binciko wata doka cikin kundin tsarin mulki da ta haramtawa 'yan Majalisar tarayya ficewa daga jam'iyyar da ta nada su kan karagar mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Kalli Bidiyon nasarar hukumar sojin

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng