Sauran ƙiris a kammala babbar hanyar Kauran Namoda zuwa Birnin Magaji a jihar Zamfara

Sauran ƙiris a kammala babbar hanyar Kauran Namoda zuwa Birnin Magaji a jihar Zamfara

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, wani babban ma'aikacin gwamnatin jihar Zamfara ya bayyana cewa, sauran ƙiris a kammala aikin titin garin Kauran Namoda, Birnin Magaji da kuma Dauran dake jihar Zamfara.

Kwamishinan na ma'aikatar kasafi da tsare-tsaren tattalin arzikin na jihar, Alhaji Ibrahim Birnin Magaji, shine ya bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai da gudana cikin Kanon Dabo a ranar Juma'ar da ta gabata.

Yake cewa, gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Abdulaziz Abubakar Yari, ta fito ƙwanta da kwarkwata tare da jajircewa wajen gudanar da wannan babban aiki sakamakon bukatar al'ummar yakunan da suka shafe shekaru aru-aru su na kiran gwamnatocin da suka shude.

Sauran ƙiris a kammala babbar hanyar Kauran Namoda zuwa Birnin Magaji a jihar Zamfara

Sauran ƙiris a kammala babbar hanyar Kauran Namoda zuwa Birnin Magaji a jihar Zamfara

Bayan tsawon shekaru kimanin 40 da suka shude, gwamna Yari ya bayyana fifikonsa a zahiri tare hangen muhimmancin wannan katafaren aiki da zai matukar bunkasa tattalin arziki a jihar.

Kwamshinan yake cewa, an kammala kaso 98 cikin 100 na wannan babban aiki da a sanadiyar haka ne gwamnatin jihar tuni ta aika da sakon ta ga shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ya kaddamar da aikin da zarar ya kammalu baki daya.

Ya ci gaba da cewa, wannan babbar hanya za ta inganta tare da taka rawar gani wajen bunkasar tattalin arziki ga al'ummar jihar da kuma makociyar jiha ta Katsina.

KARANTA KUMA: Za a ba kowane 'Dan majalisa na APC N150m domin tsige Saraki da Dogara - Timi Frank

Kazalika Birnin Magaji ya kara da cewa, gwamnatin jihar ta malalar da dukiya ta kimanin Naira miliyan 700 wajen gudanar da gyara a babban asibitin Birnin Magaji tare da samar da tsaftataccen ruwa sha ga kauyukan dake makotaka da yankin.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, Kwamishinan ya ziyarci jihar Kano ne domin halartar wai taro na inganta zamantakewar kananan yara.

A yayin haka kuma kwamishinan ya yi kira ga al'ummar jihar akan ci gaba d agoyon bayan gwamnan Abdulaziz yari da ta shugaban kasa Muhammadu domin samun karsashi na sauke masu nauyin da rataya a wuyan su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel