Sanata Wamakko da jiga jigan APC sun shirya gudanar da gangamin nunawa Tambuwal iyakar sa a Sokoto

Sanata Wamakko da jiga jigan APC sun shirya gudanar da gangamin nunawa Tambuwal iyakar sa a Sokoto

A halin da ake ciki yanzu haka dai garin Sokoto ya dauki harami inda kusan duk inda mutum ya kalla zai ga kowa na ta shire-shiren tarbar tsohon gwamnan jihar Alu Magatakarda Wamakko da sauran jiga-jigan APC a jihar da za su zo yin gangami.

Wannan dai kamar yadda muka samu, yana zuwa ne kwanaki kadan biyo bayan ficewar gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal daga jam'iyyar APC zuwa PDP a jihar.

Sanata Wamakko da jiga jigan APC sun shirya gudanar da gangamin nunawa Tambuwal iyakar sa a Sokoto

Sanata Wamakko da jiga jigan APC sun shirya gudanar da gangamin nunawa Tambuwal iyakar sa a Sokoto

KU KARANTA: Jahohi 21 da ake sa ran Buhari ya lashe a zaben 2019

Legit.ng ta samu cewa sai dai da tsohon gwamnan jihar Alu Wamakko yake tsokaci game da sauyin shekar ta sa, ya bayyana cewa yana tausaya masa kuma zai shigo garin domin ya nunawa duniya cewa jihar Sokoto ta APC ce.

A wani labarin kuma, Labarin da muke samu daga majiyar mu ta Rariya na nuni ne da cewa Honarabul Alasan Ado Doguwa, dan majalisa ne mai wakiltar Doguwa da Tudun Wada a jihar Kano ya tsallake rijiya da baya biyo bayan wani hatsarin mota da ya rutsa da shi.

Kamar yadda muka samu, hatsarin dai ya same shi ne tare da abokan tafiyar sa akan hanyar sa daga Kano zuwa Abuja amma dai ba'a samu rasa rayuka ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel