Baza mu bar 'yan kaudi su kwace mana jam'iyya ba - Makarfi

Baza mu bar 'yan kaudi su kwace mana jam'iyya ba - Makarfi

A yayin da wasu jiga jigan jam'iyyar APC suke canja sheka suna komawa babbar jam'iyyar adawa ta PDP, shi kuma tsohon gwamnan Kaduna Ahmed Makarfi yana ganin bai kamata jam'iyyar ta su ta dinga karbar kowanne mutum ba

Baza mu bar 'yan kaudi su kwace mana jam'iyya ba - Makarfi
Baza mu bar 'yan kaudi su kwace mana jam'iyya ba - Makarfi

Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma mai neman shugabancin kasa karkashin inuwar jam'iyyar PDP a zabe mai zuwa, Sanata Ahmed Makarfi ya ja kunnen shugabannin jam'iyyar PDP akan yanda take karbar masu gudowa zuwa jam'iyyar daga jam'iyyar APC.

Yayi maganar ne jiya a garin Lokoja lokacin da ya hadu da shugabannin jam'iyyar PDP a jihar Kogi domin neman goyon bayan su akan kujerar da yake nema.

DUBA WANNAN: Dalilan da suka sanya Akpabio shirin komawa APC

Yace shugabannin dole su guji kuskuren da aka tafka a lokacin da jam'iyyar take hannun Sanata Ali Modu Sheriff.

Makarfi yace: "Ana maraba da kowa amma dole mu kiyaye, dole ne mu guji ba wa baki kujerar masu gida, a barsu a matsayin su na baki, don daga samun kujerar masu gidan watarana korar masu gidan zasu yi.

"PDP bazata bar hakan ta faru ba. Su zo, su more damar su amma dole ne mu san abinda zamu iya basu da wanda zamu hana su," inji shi.

Kamar yanda yace, dole PDP tayi taka tsan-tsan gurin zaben wanda zai nemi kujerar shugabancin kasa a zaben 2019, domin yin kuskure a nan tamkar kuskure ne ga dukkan kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng