Malam Garkawy da Dalibansa zasu fito cikin koshin lafiya – Inji Sheikh Gumi

Malam Garkawy da Dalibansa zasu fito cikin koshin lafiya – Inji Sheikh Gumi

Shahararren Malamin addinin Islama dake zaune a jihar Kaduna, Malam Abubakar Mahmud Gumi ya bayyana cewa da ikon Allah, Allah zai bayyanar da Malam Ahmad Garkawy lafiya tare da dalibansa da aka yi garkuwa da su.

Legit.ng ta ruwaito Gumi ya bayyana haka ne a shafinsa na kafar sadarwar zamani, Facebook, inda yayi addu’ar Allah ya kubutar da dukkanin wadanda ake tsare dasu daga zalunci da mugunta, sa’annan yayi fatan amincin Allah a yankin Arewa gaba daya.

KU KARANTA: Manyan jiragen ruwa 35 dauke da tataccen man fetir da kayan abinci sun nufo Najeriya

Malam Garkawy da Dalibansa zasu fito cikin koshin lafiya – Inji Sheikh Gumi
Malam Garkawy

A ranar Alhamis, 2 ga watan Yuli ne wasu gungun yan bindiga suka yi awon gaba da shehin Malamin tare da dalibansa a daidai lokacin da suka tafi gonarsu, wanda suke nomawa a gefen garin Kaduna, kuma har zuwa hada wannan rahoto babu labarinsu.

“Allah kai ke da tsaro, kai ke kawo tsaro, wadanda ake ikirarin suna da tsaro suma Allah tsoro suke ji, Allah ka kubutar da duk wanda akayi garkuwa dashi, Allah ka bamu aminci da natsuwa a cikin wannan jarabawa, ka saukar da natuswa da aminci a cikin gidajen da suke cikin tashin hankali.” Inji shi.

Daga karshe Dakta ya nuna kaduwarsa kwarai da sace Al-Garkawy, inda yace har yanzu ya kasa samun nutsuwa a zuciyarsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng