Tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso ya karbi katin Jam'iyyar PDP

Tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso ya karbi katin Jam'iyyar PDP

Labari ya zo mana cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya karbi takardar sa ta zama ‘Dan Jam’iyyar PDP. Sanatan dai ya dawo Jam’iyyar da ya ci zaben Gwamna a baya a kai.

Tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso ya karbi katin Jam'iyyar PDP
Rabiu Musa Kwankwaso ya karbi katin zama 'Dan PDP

A jiya ne Jam’iyyar adawa ta PDP ta shirya babban taron ta na Majalisar zartarwa watau NEC inda irin su Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso da sauran wadanda su bar APC su ka halarta.

Manyan ‘yan siyasar da su ka bar Jam’iyyar APC su ka koma PDP kwanan nan sun halarci taron na NEC da aka shirya a babban Birnin Tarayya Abuja. A nan ne aka ba Sanata Rabiu Musa Kwankwaso katin zama cikakken ‘Dan Jam’iyya.

KU KARANTA: Wani babban ‘Dan PDP a ya koma APC bayan an mika PDP hannun Saraki

Tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso ya karbi katin Jam'iyyar PDP
Haruna Umar Doguwa ya ba Kwankwaso katin PDP

Sanatan ya nuna farin cikin sa na dawowa jam’iyyar sa ta asali wanda yayi takarar Gwamnan Kano a 1999 da kuma 2011 a cikin ta. Rabiu Kwankwaso yayi kira da sauran ‘Ya ‘yan Jam’iyyar adawar kasar da su dage wajen ganin Najeriya ta cigaba.

Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Kano watau Alhaji Haruna Umar Doguwa ne ya mikawa tsohon Gwamnan katin na sa. Bisa dukkan alamu Sanatan na Kano tsakiya Rabiu Musa Kwankwaso zai nemi takarar Shugaban kasa a PDP a zabe mai zuwa.

Jiya kun ji cewa twani tsohon Kwamishinan harkokin gidan Gwamnati Aminu Abdussalam ya bayyana cewa irin saba alkawarin da da Gwamnatin nan ta Shugaba Buhari ta yi ne ta sa su ka bar Jam’iyyar APC mai mulki su ka dawo Jam’iyyar PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng