Har yanzu ina tare da Baba Buhari – Inji Minista Aisha Alhassan

Har yanzu ina tare da Baba Buhari – Inji Minista Aisha Alhassan

Ministan kula da harkokin Mata da ayyukan cigaba, Hajiya Aisha Alhassan wanda aka fi sani da suna Mama Taraba ta musanta batun da ake yadawa na cewa wai ta yi murabus daga mukaminta tare da ficewa daga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito ta musanta wannan batu, inda tace wannan wasikar dake yawo a kafafaen sadarwar zamani ta rubuta shi ne a ranar 27 ga want Yuli, ta rubuta shi ne kawai da nufin bayyana ma shugaba Buhari burinta na sake tsayawa takarar gwamna a jihar Taraba a zaben 2019.

KU KARANTA: Ramin karya kurarre ne: Manyan ayyukan gwamnatin tarayya guda 17 a jihar Sakkwato

Har yanzu ina tare da Baba Buhari – Inji Minista Aisha Alhassan
Minista Aisha Alhassan

Sai dai Mama ta kara da cewa za ta yi murabus daga mukaminta na minista a cikin watan Disamba, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar, da yace duk mai rike da mukami, kuma yana bukatar tsayawa takara toh ya ajiye mukaminsa kwanaki Talatin kafin zabe.

Daga karshe Ministar ta yi fatali da yamadidin da ake yadawa na cewa ta bata da shugaba Buhari, kuma bata tare da shi, inda tace: “Har yanzu ina tare da shugaba Buhari, kuma ni minstace a gwamnatinsa.”

Idan za’a tuna, a zaben shekarar 2015, Aisha Alhassan ta fafata a takarar gwamnan jihar Taraba a inuwar jam’iyyar APC, inda ta zo ta biyu, yayin da dan takarar PDP Darius Ishaku ya lashe zaben.

Haka zalika wasikar dake yawo na martanin da shugaba Buhari ya aika ma Aisha baya nufin yana goyon bayanta, illa yana bayyana goyon bayansa ga burinta na tsayawa takarar gwamna jihar, tare da tabbatar mata da cewa hukumar zabe za ta yi adalci ga dukkanin yan takarkaru.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel