Kishi kumallon mata: Uwargida ta guntule ma Maigida mazakuta saboda ya fi kula da Amarya

Kishi kumallon mata: Uwargida ta guntule ma Maigida mazakuta saboda ya fi kula da Amarya

Wata Mata ta fada komar Yansandan kasar Indiya biyo bayan kamata da laifin guntule ma Maigidanta mazakutarsa sakamakon zarginsa da take yi shankatakewa a dakin Amaryar da ya karo, ita kuma yana shanyata kamar kayan wanki.

Rahotanni daga kamfanin dillancin labaru, NAN, sun tabbatar da faruwar wannan mummunan lamari a ranar Alhamis, 2 ga watan Yuli, inda Matar ta aikata wannan danyen aiki ga Maigidanta bayan kaurewar musu a tsakaninsu, da ya kai ga baiwa hammata iska.

KU KARANTA: Farfesa Hafiz ya karyata batun yin murabus daga mukamin mataimakin Ganduje

Majiyar Legit.ng ta ruwaito tuni aka garzaya da Yunus Ahmed zuwa babban Asibitin Uttar Pradesh dake lardin Muzaffarnagar, yayin da aka Yansanda suka yi ram da Uwargida, inji wani jami’in Dansanda Anil Kaparwan.

Kaparwan yace wannan rikici ya samo asali ne tun a shekarar 2017, inda Yunus Ahmed ya karo Mata sakamakon Uwargidar bata taba haihuwar Da Namiji ba, toh amma aka dinga samun matsaloli tsakaninsa da Matar duk da cewa sai da ya nemi izininta kafin ya kara auren.

“Ita dai Matar ta dade tana zargin Mijin da wancakalar da ita da yaranta, tare da shantakewa a dakin Amarya, har sai a ranar Larabar nan, inda ta yi amfani da wuka ta yanke masa mazakuta yayin da rikici ya kaure a tsakaninsu.” Inji Dansandan.

Daga karshe Dansandan yace “A yanzu haka mun kama Matar, bayan yan uwan Mijin sun shigar da kara wajen Yansanda, shi kuma yana cikin mawuyacin hali a Asibiti, amma yana samun kulawar data dace.”

Ana tuhuma matar da cutar da jikin dan Adam tare da yi masa mummunan rauni, kuma wannan laifi na tattare da hukuncin zaman gida Yari na tsawon shekaru goma babu kakkautawa, a kasar India.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng