Ramin karya kurarre ne: Manyan ayyukan gwamnatin tarayya guda 17 a jihar Sakkwato

Ramin karya kurarre ne: Manyan ayyukan gwamnatin tarayya guda 17 a jihar Sakkwato

A ranar Laraba, 1 ga watan Agusta ne gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya yi fatali da jam’iyyar APC, inda ya rungumi jam’iyyar PDP, inda ya bayyana gwamnatin shugaba Buhari a matsayin wanda bata da aldaci, tare da rashin iya salon mulki.

Haka zalika Legit.ng ta ruwaito Tambuwal ya zargi gwamnayin APC da rashin kawo wani aikin cigaba ko da guda daya ne a jihar Sakkwato, kuma ta yi watsi da ayyukan gwamnatin tarayya da gwamnatocin baya suka fara, bata karasa su ba.

KU KARANTA: Buhari ya tubure sai Saraki ya sauka daga mukamin shugaban majalisar Dattawa

Sai dai wani masanin al’amuran yau da kullum, kuma ma’abocin kafar sadarwar Facebook, Aliyu Abdullahi ya karyata zargin rashin tabuka komai a jihar Sakkwato ga gwamnatin tarayya, kamar yadda Tambuwal ya fada, inda ya lissafa ayyuka goma sha bakwai da Buhari ya yi a jihar;

1- Lamunin kudin Paris ga jihar Sakkwato na naira biliyan goma sha takwas da miliyan dari uku (N18.3bn)

2- Kudin tallafi ga jihar Sakkwato don gudanar da kasafin kudinta

3- Tallafin naira biliyan goma da miliyan Tara (N10.09bn) ga jihar Sakkwato don biyan Albashi da Fansho

4- Tallafin tafiyar da harkar noma na naira biliyan Takwas da miliyan dari bakwai (N8.7bn) ga jihar Sakkwato

5- Sake gina babbar hanyar Runjin Sambo har zuwa cikin jami’ar Usmanu Danfodiyo

6- Sake gina babbar hanyar Sakkwato – Tambuwal- Jega

7- Kafa sabuwar sabuwar rundunar Soji ta 8 a garin Kalambaina

8- Aikin madatsar ruwan Shagari don sawwaka noman rani

9- Aikin babbar hanyar da ta hada Sabon Birni – Tsululu – Kuya – Maradi

10 – Aikin dakatar da zaizayar kasa a kauyukan Dogon Daji, Bashir da Jabo duk a karamar hukumar Tambuwal

11- Aikin samar da cibiyar kasuwanci ta jihar Sakkwato

12- Daukan matasa sama da 2,200 daga jihar Sakkwato

13- Bada umarnin gina katafaren Asibitin koyarwa na Sojoji a jihar Sakkwato, da babu irinsa a Najeriya

14- Tallafin naira biliyan biyu na magance yanayi (Ecolgical fund)

15- Gina sabbin gidaje 80 a Kwannawa

16- Tallafin dala miliyan daya da dubu dari biyar don inganta kiwon lafiya

17- Aikin dakatar da zaizayar kasa a karamar hukumar Sakkwato ta kudu.

Da wannan sai mai karatu ya yi shari'a idan Buhari ya yi aiki a Sakkwato ko A'a.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng