Ina nan tare da Mai gidana a APC - Direban Lai Mohammed

Ina nan tare da Mai gidana a APC - Direban Lai Mohammed

Aliyu Omeiza, direban ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya musa rahoton da kafafen yada labarai ke bazawa na cewa ya gudu bar Mai gidansa akan titin Abuja ya bi guguwar jam'iyyar PDP

Ina nan tare da Mai gidana a APC - Direban Lai Mohammed

Ina nan tare da Mai gidana a APC - Direban Lai Mohammed

Aliyu Omeiza, direban ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya musa rahoton da kafafen yada labarai ke bazawa na cewa ya gudu bar Mai gidansa akan titin Abuja ya bi guguwar jam'iyyar PDP.

A wata tataunawar waya da ofishin dillancin labarai suka yii dashi a ranar Larabar nan data gabata, Omeiza yace rahoton na karya ne saboda hakan bai faru ba.

DUBA WANNAN: Wata Sabuwa: Kotu ta sakawa El-Rufai doka akan rikicin sa da Sanata Hunkuyi

"Karya ce, abu makamancin haka bai faru ba. Na tuka maigidana zuwa fadar shugaban kasa da safe domin halartar taron zababbun jami'an gwamnatin tarayya.

"Mun kuma je gurare da yawa, kafin in tashi aiki.

"Ni ba dan siyasa bane, bana wata jam'iyyar siyasa balle in canza jam'iyya.

"Wannan shine misalin labarun karya da maigidana yake yawan magana akai," inji shi.

Omeiza yace ya kasance direban ministan na shekaru da dama, bashi kuma da dalilin barin ministan saboda yana kyautata mishi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel