Farawa da iyawa: Mataimakin Gwamnan jihar Sakkwato ya barranta da Gwamna Tambuwal

Farawa da iyawa: Mataimakin Gwamnan jihar Sakkwato ya barranta da Gwamna Tambuwal

A wani mataki irin na Angulu ta koma gidanta na tsamiyy ne a ranar Laraba, 1 ga watan Agusta gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya sauka sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP, sai dai tafiyar tasa ta bar baya da kura.

Sai dai Legit.ng ta samu rahoton dake bayyana cewa mataimakin gwamnan jihar, Ahmad Aliyu Sokoto ya yi tirjiya, inda yace ba zai bi Tambuwal zuwa jam’iyyar PDP ba, tare jaddada goyon bayansa ga jam’iyyar APC.

KU KARANTA: Shehu Sani a neman kariyar Allah daga sharrin masharranta da hassadan mahassada

Shafin ‘Sakkwato Birnin Shehu’ na kafar sadarwar zamani na Facebook ne ta bayyana haka, inda tace Ahmad Aliyu ya dauki alwashin zama abokin takara ga duk wanda ya samu tikitin takarar gwamnan jihar a inuwar jam’iyyar APC a zaben 2019.

Bugu da kari, mataimakin gwamna Ahmad ya jaddada goyon bayansa ga shugabancin Muhammadu Buhari, da kuma jagoransa, Sanata Aliyu Magatakarda Wammako, ya kara da cewa ba zai baiwa jama’an Sakkwato kunya ba.

Shi kuwa jagoran siyasar jihar, kuma tsohon gwamnan jihar, Sanata Aliyu Wammako yace lallai kaddara ta hau Tambuwal, don kuwa Sakkwatawa shi suke goyon baya, don haka yana da tabbacin zasu kada Tambuwal a zaben 2019.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel