Tabargaza: Magidanci ya saka tabarya ya buge matar sa har lahira

Tabargaza: Magidanci ya saka tabarya ya buge matar sa har lahira

’Yan sanda a jihar Anambra sun cafke wani magidanci, James Nworah, bisa tuhumarsa da kisan matar sad a sanyin safiyar yau, Talata.

Lamarin ya faru ne a gidansu dake lamba 2 kan titin Umudioka a garin Ngbuka Nkpor ta karamar hukumar Idemili ta arewa.

Ma’auratan masu ‘ya’ya 5; maza uku, mata biyu basu dade da tarewa a gidan da lamarin ya faru ba.

Wasu da suka san Nworah sun bayyana shi a matsayin mai tabin hankali da a baya yake sana’ar acaba kafin a hana sana’ar.

Tabargaza: Magidanci ya saka tabarya ya buge matar sa har lahira
Magidancin da ya saka tabarya ya buge matar sa har lahira

Tabargaza: Magidanci ya saka tabarya ya buge matar sa har lahira
Magidanci ya saka tabarya ya buge matar sa har lahira

Sabani ya shiga tsakanin ma’auratan ne da misalign karfe 2 na dare bayan sun kamala tatar gasar koko da suke sayarwa.

A cewar makwabtansu, matar, Jennifer Nworah, ta je ta kwanta bayan rikicin da suka yi amma daga baya sai Nworah ya dauki tabarya ya bi ta daki ya yi ta jibga tamkar mai bugun shinkafa.

DUBA WANNAN: Tsige Bukola: Shugabancin APC da Sanatocin jam'iyyar sun gana da Buhari

Shaidun sun bayyana cewar Nworah ne da kansa ya kira dan uwansa ya shaida masa cewar ya kasha matar sa kafin da safe jami’an ‘yan sanda su kama shi.

Shugaban rundunar ‘yan sanda ta ofishin Ogidi, CSP Mark Ijafaru, ya tabbatar da afkuwar lamarin tare da sanar da cewar zasu mayar da Nworah sashen bincike na musamman.

Tabargaza: Magidanci ya saka tabarya ya buge matar sa har lahira
Magidanci ya saka tabarya ya buge matar sa har lahira

Tabargaza: Magidanci ya saka tabarya ya buge matar sa har lahira
Magidanci ya saka tabarya ya buge matar sa har lahira

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng