Tuwon girma: PDP ta shirya liyafar karrama ‘ya’yanta da suka dawo daga APC, hotuna
A wata sanarwa da jam’iyyar adawa ta PDP ta fitar a shafinta na Tuwita, ta bayyana cewar ta shirya wata liyafa ta musamman domin karrama duk wadanda suka dawo cikinta daga cikin jam’iyyar APC a Otal din Transcorp dake Abuja.
A satin da ya gabata ne wasu mambobin majalisar dattijai 15 da na majalisar wakilai fiye da 30 suka fice daga jam’iyyar APC tare da komawa PDP. Kazalika a cikin satin ne gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya fita daga APC tare da komawa APC.
Ficewar ‘ya’yan jam’iyyar APC zuwa PDP ta cigaba a cikin satin nan da muke ciki da fitar shugaban majalisar dattijiai, Bukola Saraki, da gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, a ranar Talata.
DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya ziyarci ofishin kamfen dinsa na kasa, duba hotuna
A ranar Laraba kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, da mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar, sun kara canja sheka daga APC zuwa PDP.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng