Dubunnan mutane sun samu aikin N-Power a jihar Kano

Dubunnan mutane sun samu aikin N-Power a jihar Kano

- Mutane 12,000 ne suka samu nasarar samun aikin N-Power

- An fito da tsarin ne don rage rashin aikin yi a fadin kasar nan

- Hajiya Aisha tayi kira ga wadanda suka samu nasarar samun aikin da suyi aiki ta hanyar daya kamata.

Dubunnan mutane sun samu aikin N-Power a jihar Kano
Dubunnan mutane sun samu aikin N-Power a jihar Kano

Matasa 12,000 ne a jihar Kano suka samu nasarar samun aikin N-Power wanda gwamnatin tarayya ta fito dashi dan rage rashin aikin yi a fadin kasar nan.

Kwamishinar kudi da tsare-tsare ta jihar Kano, Hajiya Aisha Jafar Yusuf ce ta bayyanawa manema labarai hakan a yau Larabar nan a jihar ta Kano.

DUBA WANNAN: Al'umma masu son cigaba: Sun tarawa kasar su taimakon dala miliyan 41 a cikin wata biyu, don ta biya bashin da ake binta

Tace za'a kafe sunayen wadanda suka samu nasarar a kananan hukumomi 44 dake fadin jihar.

"A yayin tsari na farko daya gudana matasa 23,000 kadai sukayi rigista inda aka samu cigaba a zagaye na biyu matsa 60,000 sukayi rigista."

Daga cikin matasa 60,000 da sukayi rigistar matasa 12,000 ne suka samu nasara.

Jafar Yusuf tayi kira ga wadanda suka samu shiga tsarin dasuyi amfani dashi ta hanyar daya kamata.

Gwamnatin tarayya ta bijiro da tsarin ne don rage rashin aikin yi da ake fama dashi a kasar nan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel