Yadda wasu yan majalisa Mata suka baiwa hammata iska saboda Namiji

Yadda wasu yan majalisa Mata suka baiwa hammata iska saboda Namiji

Wasu manyan Mata biyu yan majalisar dokokin kasar Kenya sun baiwa hammata iska a wani gidan cin abinci bayan da cacar baki ta kaure a tsakaninsu akan wani dan saurayi da dukkaninsu suke kauna.

Wannan rikici ya faru ne a ranar Talata, a wnai gidan abinci yayin da guda ta fado cikin dakin abincin bayan ta samu labarin saurayinsu guda da dayar yar majalisa, anan ne fa kowannensu ya fara ikirarin wannan saurayi nasa ne.

KU KARANTA: Yaki da Boko Haram: Rundunar Sojojin Najeriya ta hada kai da mafarauta da yan tauri

Fadawarta cikin gidan cin abincin keda wuya da kuma yadda shiga tana hucin bacin rai da nufin yi ma kishiyarta rashin mutunci, dayar ta sha jinin jikinta, inda ta fara ihu tana cewa “Ku taimaki wannan Matar bata da lafiya, tana bukatar taimako.”

Da kyar aka shawo kan yan majalisun, inda jami’an tsaron majalisar dokokin kasar suka rabasu amma fa bayan sun yi ma kansu jina jina, sai dai zuwa yan shugabancin majalisar sun fara gudanar da bincike game da lamarin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel