Kudi a kashe su ta hanya mai kyau: Babban Bankin Najeriya yayi gargadi ga 'yan kasuwa su daina wulakanta kudi

Kudi a kashe su ta hanya mai kyau: Babban Bankin Najeriya yayi gargadi ga 'yan kasuwa su daina wulakanta kudi

- Babban bankin Najeriya zai fara gabatar da wani tsari domin yan kasuwa.

- Yayi kira ga mutane dasu daina cukwikuye kudi da kuma yin rubutu a jiki

- Duk wanda aka kama da laifin wulakanta naira akwai hukunci a kansa.

Kudi a kashe su ta hanya mai kyau: Babban Bankin Najeriya yayi gargadi ga 'yan kasuwa su daina wulakanta kudi
Kudi a kashe su ta hanya mai kyau: Babban Bankin Najeriya yayi gargadi ga 'yan kasuwa su daina wulakanta kudi

A ranar Talatar nan ne babban bankin Najeriya CBN ya fara gabatar da wani tsari domin yan kasuwa maza da mata a jahar Ondo na yanda zasuyi aiki da bankin kasuwanci ba tare da wani jinkiri ba

A yayin baje kolin bankin yaja kunnen yan kasuwar akan yanda ake wulakanta kudi.

Mataimakin Darakta na fannin harkokin kudi na babban bankin Najeriya Mr Benedict Maduagwu yace ya kamata al'umma su san yanda ya kamata su dinga tafiyar da harkokin kudi a cikin al'umma.

DUBA WANNAN: Duniya ina zaki damu: Ta gwammace ta aika shi lahira, data bari ya duba wayarta

Maduagwu ya kara da cewa duk wanda aka kama yana wulakanta Naira zaiyi zaman gidan yari na shekara biyar ko ya bayar da tarar naira dubu hamsin.

Yace "Gwamnati tana amfani da kudin haraji don a fitar da Naira to bai kamata ace muna wulakanta nairar ba, wanda hakan zai kaimu ga bawa bankin kasuwanci bashi wanda zai kawo nakasu a tattalin arzikin mu.

"Karku dinga cukwikuye kudi dayin rubutu a jikinta sannan a dena sanya kudi a cikin jiki don gudun kamuwa da wani ciwo".

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel