Dandalin Kannywood: Siffofin namijin da zan iya aure - Halima Atete
Daya daga cikin fitattun fuskukoki a masana'antar Kannywood da tauraruwar ta ke haskawa ba tun yau ba watau Halima Atete ta bayar da sifofin namijin da tace zata iya aure idan har Allah ya kawo mata lokacin.
Jarumar dai ta bayyana hakan ne a lokacin da take fira da wakiliyar majiyar mu ta Daily Nigerian inda take ansa tambayoyi akan abubuwan da suka shafi rayuwar ta ta fili da kuma ta wasan kwaikwayo.
KU KARANTA: Sanusi Lamido ya caccaki gwamnatin Buhari
Legit.ng ta samu cewa da aka tambayi jarumar ko waye zata aura sai ta ce wannan sirri ne da ta barwa zuciyar ta kadai kuma bata son fadar sa yanzu har sai lokaci yayi.
Amma da wakiliyar majiyar ta mu ta tambaye ta ko zata zayyana irin sifofin wanda take so ta aura din, jaruma Halima Atete sai ta kada baki tace ita gaskiya bata son namiji mai fuska biyu - watau ma'ana wanda bai da gaskiya kuma mayaudari.
Haka nan kuma ta ce ita tana da matukar kishi amma ba zata damu ba koda yana da aure zata iya auren sa idan dai har ba mayaudari bane.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng