Yar uwar Bukola Saraki ta jaddada goyon bayanta ga shugaba Buhari

Yar uwar Bukola Saraki ta jaddada goyon bayanta ga shugaba Buhari

Kanwar shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, mai suna Gbemisola Rukayya Bukola Saraki ta bayyana barranta da matakin da Saraki ya dauka na ficewa daga jam’iyyar APC, tare da jaddado goyon bayan ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Rukayya, wanda itace tsohuwar Sanata mai wakiltar al’ummar Kwara ta tsakiya a majalisar dattawa, wanda a hannunta Saraki ya kwace kujerar bayan ya kammala wa’adinsa a matsayin gwamnan jihar Kwara, kamar yadda Legit.ng ta samu rahoto.

KU KARANTA: Jaraba: Yadda wasu matasa su 8 suka yi ma wata Akuya fyade yayin da take dauke da ciki

Rukayya tace tana goyon bayan Buhari dari bisa dari a kokarinsa na sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019, tare da burin ganin jam’iyyar APC ta yi nasara a jihar Kwara, da sauran jihohin Najeriya.

Tsohuwar Sanatan ta bayyana cewa ta sadaukar da dukkanin kungiyoyinta na siyasa guda shidda ga samun nasarar APC da na shugaban kasa Muhammadu Buhari, duk da ficewar Saraki da gwamnan jihar Kwara Abdulfatah Ahmed daga APC.

Yar uwar Sanata Bukola Saraki ta kara da cewa siyasa ya ta’allaka ne ga yi ma jama’a aiki, do haka tace ya zama wajibi a gudanar da tsaftatacciyar siyasa, cikin kwanciyar hankali tare da ganin mutuncin juna.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng