Adadin layukan wayoyin Salula a Najeriya sun kai miliyan 162.3

Adadin layukan wayoyin Salula a Najeriya sun kai miliyan 162.3

Hukumar kula da kamfanonin sadarwa ta Najeriya, NCC, ta bayyana adadin layukan wayar salula, wato SIM Card da ake amfani dasu a Najeriya sun tasan ma guda dai dai har miliyan dari da sittin da uku da dubu da dari uku, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

NCC ta bayyana haka ne a shafinta na yanar gizo, inda ta bayyana adadin layukan waya dake ake amfani dasu a Najeriya a zuwa watan Yunin daya gabata sun kai 162,300,000, hakan ke nuna karuwarsa daga 162,070,000 a watan Mayu, hakan ke nufin an samu karuwar sabbin layuka 232,230 a watan guda.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta mayar da yan Najeriya tamkar mazauna gidan Yari - Tambuwal

Majiyar Legit.ng ta ruwaito su kuwa layukan CDMA a Najeriya suna nan a dubru dari biyu da dari biyar da sittin da shida, yayin da kayyadaddun layuka suka suka karu daga 137,010 a watan Mayu zuwa 140,627 a watan Yuni.

layukan wayoyin Salula
Adadin layukan wayoyin Salula a Najeriya sun kai miliyan 162.3

Sai kuma sabbin layuka, wanda hukumar NCC tace sun ragu daga 140,259,751 a watan Mayu zuwa 239,339,812 a watan Yuni, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Ko a kwanakin baya sai da yan Najeriya suka yi ta musayar ra’ayi game da yadda hukumar NCC ta dauki ma’aikata ta kofar baya ba tare da sanar ma yan Najeriya ba, wanda hakan ke nufin ana baiwa yayan masu uwa a gindin murhu fifiko.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng