Manyan Jam'iyyar PDP sun yi maraba da dawowar Rabiu Kwankwaso Jam’iyya
Mun ji labari cewa wani daga cikin manyan ‘Yan Jam’iyyar adawa watau PDP a Jihar Kano wanda yana cikin manya a da a ANPP yayi murna da dawowar tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso cikin Jam’iyyar da ya bari kafin zaben 2015.
Abdullai Sani Rogo wanda tsohon Kwamishina ne a Jihar Kano a lokacin Gwamnatin ANPP yayi murnar dawowar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Magoya bayan sa cikin PDP inda yayi addu’a sauyin shekan ya zama alheri a zabe mai zuwa.
Sani Rogo wanda yayi aiki da tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau ya karyata rade-radin cewa ya fice daga PDP ya koma APC. Rogo ta bakin mai magana da yawun sa watau Muhammad Bashir Amin yace yana nan a Jam’iyyar ta PDP har gobe.
KU KARANTA: Ni da Kwankwaso ne iyayen PDP a Kano Inji Shekarau
Bayan nan ma dai Bashir Aminu wanda shi ne Shugaban yakin neman zaben ‘Dan takarar Gwamnan Jihar Kano a karkasin PDP Salihu Sagir Takai a kasafen yada labarai na zamani ya bayyana cewa Takai yana maraba da Mutanen Kwankwaso.
‘Dan takarar Gwamnan na PDP yace dama Jam’iyyar su a shirya ta ke ta karbi Jama’a inda yace PDP kamar kofar Sabon Gar ice inda kowa ke iya shigowa a ko yaushe. Takai ya bayyana wannan ne wajen wani taron siyasa da aka yi kwanan nan.
Jiya kun ji cewa daya daga cikin masu ba Gwamnan Kano Dr. Umar Abdullahi Ganduje shawara ya tona asirin wasu badakaloli da ake zargin tsohon Gwamnan na Jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso da su a lokacin yana rike da mulki.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng