Ruwa ba ya tsami banza: Da hannun tsofin gwamnonin PDP a rikicin makiyaya da manoma – Binciken Turai

Ruwa ba ya tsami banza: Da hannun tsofin gwamnonin PDP a rikicin makiyaya da manoma – Binciken Turai

Akwai alamu masu karfi dake nuna cewar akwai hannun tsofin gwamnonin jam’iyyar PDP a rikicin manoma da makiyaya da ya ki ci - ya ki cinyewa a wasu sassan kasar nan, kamar yadda wani rahoton wata kungiyar Turai, “The Bridge Centre”, ya sanar.

A cewar rahoton, akwai yiwuwar cewar wasu daga cikin jagororin jam’iyyar PDP na daurewa kashe-kashen gindi domin ganin sun durkusar da gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki.

Rahoton ya kara da cewa idan aka lura, kashe-kashen da ake yi a Najeriya na faruwa ne a sassan da ba a zabi jam’iyyar PDP ba.

Wani misali da rahoton ya bayar shine yadda aka taba kama wani mai suna “Gana” daya daga cikin masu jagorantar kashe-kashe a jihar Benuwe da kuma ya ke da alaka da wani tsohon gwamna da ya yi mulki tsakanin 2007 zuwa 2015.

Kazalika rahoton ya bayyana yadda gwamna Ortom ya kasa daukan mataki a kan maganar Gana saboda alakar shi da tsohon gwamnan.

Ruwa ba ya tsami banza: Da hannun tsofin gwamnonin PDP a rikicin makiyaya da manoma – Binciken Turai
Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe

Shugaban bangaren bincike da adana bayanai na kungiyar, Elizabeth Robertson, ya yi kira ga hukumar tsaro ta yankin Turai da ta gaggauta shiga cikin batun rikicin makiyaya da manoma a Najeriya kafin lamarin ya zama matsala ga duniya bakidaya.

DUBA WANNAN: Zaluncin 'yan sanda, bama so!: Direbobi sun yiwa 'yan sanda zanga-zanga a Maiduguri

Kungiyar ta nemi a gaggauta gudanar da bincike a kan wasu jagororin jam’iyyar PDP musamman tsofin gwamnoni dangane da rawar suke takawa wajen rura wutar rikicin makiyaya da manoma domin cimma wata manufa ta siyasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel