Zaluncin ‘yan sanda! Bama so!: Ana yiwa ‘yan sanda zanga-zanga a Maiduguri
Direbobin babur mai kafa uku da ake kira “a daidaita sahu ko keke Napep” na can a garin Maiduguri, babban birni jihar Borno, suna gudanar da wata zangar-zangar nuna kin amincewa da yadda jami’an ‘yan sanda ke matsa masu basu nagoro.
Direbobin, yawancinsu matasa, sun fito kan titi dauke da sako rubuce a takardu na nuna cewar jami’an ‘yan sanda na zaluntar su.
A daya daga cikin hotunan da zaku iya gani, wani direba ne dauke da babbar takarda an rubuta “zaluncin ‘yan sanda, bama so”, yayin da wasu kuma daga cikin direbobin na rera wakar “zaluncin ‘yan sanda, bama so” tamkar a cikin shirin Indiyar Hausa.
An dade ana fama da matsalar karbar nagoro da jami’an ‘yan sanda ke yi a hannun direbobi a kan titunan cikin birane da kewayen Najeriya. A wasu lokutan har harbi jami’an ‘yan sanda ke yi domin razana direbobi su bayar da nagoro yayin da a wasu lokutan ma ake samun asarar rai idan lamari ya lalace tsakanin direbobin da jami’an ‘yan sandar.
DUBA WANNAN: 2019: Jerin gwamnonin APC 4 dake takarar kujera Sanata
Borno na fama da rikicin 'yan kungiyar Boko Haram da ya durkusar da harkokin kasuwanci a jihar, musamman a garin Maiduguri, babban birnin jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng