Kashe-kashen Zamfara: Ba rikicin Makiyaya da Manoma ba ne – Dr. Siddique Mohammed

Kashe-kashen Zamfara: Ba rikicin Makiyaya da Manoma ba ne – Dr. Siddique Mohammed

A jiya da dare ne mu ka samu labari cewa Gwamnatin Tarayya ta aika Sojoji domin kawo karshen kisan da ake yi a Garin Zamfara inda aka tashi Garuruwa da dama aka kuma kashe Bayin Allah.

Wani rikakken masani a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya wanda kuma yayi bincike a kan lamarin tsaron kasar musamman a Arewa ya bayyana bambancin rikicin Boko Haram da kuma kashe-kashen da ake yi a Garin Zamfara da kewaye.

Kashe-kashen Zamfara: Ba rikicin Makiyaya da Manoma ba ne – Dr. Siddique Mohammed

Wani rikakken Farfesa yace akwai karancin Jami'an tsaro a Najeriya

Dr. Abubakar Siddique Mohammed ya bayyana cewa daga cikin bambancin Boko Haram da masu hallaka jama’a a Zamfara shi ne rashin tarewa a Gari. ‘Yan Boko Haram su kan karbe Gari idan sun ci sa da yaki, su nemi su kafa daular su.

Bayan nan kuma Siddique Mohammed ya nuna cewa wadanda ke ta’asa a Yankin Zamfara ba su da alaka da wani addini. ‘Yan ta’addan Boko Haram na ikirarin Musulunci da kuma kafirta sauran jama’an da ba su yarda da irin akidun su ba.

Babban Masanin yace ‘Yan Boko Haram na kafa Hukuma da Gwamnatin su ne a cikin Gari yayin da Masu kashe jama’a a Zamfara kuma su ke cikin Daji a boye. ‘Yan Boko Haram na neman a bi irin addinin su inda su kuma wadannan babu ruwan su.

KU KARANTA: Jama'a sun kai kuka wajen Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Abubakar Siddique Mohammed ya nuna cewa ba rikici ba ne tsakanin Makiyaya da Manoma yake faruwa a Zamfara domin kuwa a yanzu kusan duk an karbe gonakin manoman kuma an sace shanu don haka wasu ne kurum ke kashe mutane babu dalili.

Dazu kun ji cewa wasu manyan Sanatocin da ke Arewa sun koka game da rikicin na Zamfara. Sanatan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani yayi tir da wannan abu da yake faruwa inda ya nemi Jami’an tsaro su cigaba da himma da kwazo wajen kare al’umma.

Kawo yanzu dai an fatattaki sama da mutum 12000 daga Zamfara wanda Malamin Jami’an yake ganin akwai matsalar karancin ‘Yan Sanda da kuma matsalar tsarin Jami’an tsaro a Kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel