Nahiyar Turai ta baiwa El-Rufai tallafin naira biliyan 4.2 don kammala wani muhimmin aiki
Kungiyar kasashen Turai ta baiwa gwamnatin jihar Kaduna, a karkashin jagorancin Gwamna Malam Nair Ahmad El-Rufai kyautar kudi yiro miliyan goma, kwatankwacin naira biliyan hudu da miliyan dari biyu da dubu shida da bakwai da dari bakwai da saba’in da sittin d biyu, N4204607762.4.
Daily Nigerian ta ruwaito kungiyar tare da hadin kan kasashen yammacin Afirka sun baiwa gwamnatin wannan jiha ne domin ta samu damar kammala aikin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana.
KU KARANTA: Wata Kotu ta tasa keyar yan fashi da makami guda 3 dake fakewa da sana’ar Achaba
Majiyar Legit.ng ta ruwaito hadimin gwamna El-Rufai a bangaren samar da wutar lantarki, Dolapo Popoola ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 26 ga watan Yuli a yayin rattafa hannu kan yarjejeniyar da zata samar da wadannan kudade.
“Wannan rattafa hannu zai fadada aikin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana da gwamnatin jihar ke yi zuwa ga Asibitocin jihar dake yankin kauyuka da makarantun Sakandari, kananan dakunan karbar magani da kuma cibiyoyin tace ruwan sha, domin inganta harkar ilimi da kiwon lafiya a yankunan karkara.” Inji ta.
Haka zalika gwamnatin ta shiga wata yarjejeniya tsakaninta da kungiyar kasashen Turai da cibiyar samar da cigaba na kasar Ingila don a ranar Alhamis din da ta gabata, don kulawa da wutar mega watt ta 1.7 da za’a samar daga hasken rana.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng