Gwamnonin APC 4 dake takarar kujerar Sanata

Gwamnonin APC 4 dake takarar kujerar Sanata

Majalisar dattijai, ita ce majalisa mafi girma da karfin iko a cikin majalisun tarayya guda biyu da Najeriya ke da su.

Kamar yadda sunanta ya nuna, majalisar dattijai azure ne da ‘yan kasa da suka samu gogewar aiki ke zuwa domin kirkirar dokoki da kuma sa ido a kan harkokin bangaren zartarwa domin hada karfi wajen kawo wa kasa da ‘yan kasa cigaba ta hanyar tabbatar da romon dimokradiyya ya ratsa kowanne lungu da sako.

Sai dai wani abu da yake neman zama al’ada a majalisar dattijan Najeriya, shine yadda tsofin gwamnoni suka mayar da ita wani wurin ritaya bayan kamala zangonsu na mulkin jihohi.

Ba laifi bane a tsarin dokar kasa ga gwamna ya tafi majalisar ta dattijai, inda gizo ke sakar shine; su irin wadannan tsofin gwamnoni da ke zuwa majalisar dattijai basa iya taka wata rawar gani ta fuskar kirkirar dokoki da zasu inganta rayuwar jama’ar da suke wakilta balle har su kai ga sun yi dokokin da zasu taimaki kasa baki daya.

Gwamnonin APC 4 dake takarar kujerar Sanata

Gwamnonin APC

A yanzu haka akwai tsofin gwamnoni 15 daga jihohi da jam’iyyu daban-daban a majalisar dattijan Najeriya.

Bayan wadannan adadi dake majalisar akwai wasu gwamnoni 4 daga jam’iyyar APC dake burin zarcewa zuwa majalisar dattijai daga gidajen gwamnatin jihohinsu

2. Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha: Tuni ya bayyana cewar zai tsaya takarar Sanata bayan karewar zangonsa na biyu a matsayin gwamna. Zai yi takarar ne a jam’iyyar sat a APC.

DUBA WANNAN: Kashin 'yan ta'dda ya bushe: Buhari ya tura tawagar jami'an tsaro mai karfi zuwa jihar Zamfara

Gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura: An fara zabarsa gwamna a shekarar 2011 kuma zai gama zangonsa na biyu a shekarar 2019. Shi ma ya sanar da burinsa na zama Sanata a jam’iyyar APC.

2. Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima: Zai kamala zangonsa na biyu a shekarar 2019 kuma shi ma burinsa shine ya tafi majalisar dattijai. Tuni an fara kafa allunansa na talla a birnin Maiduguri.

1. Gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Geidam: Sabanin ragowar gwamnonin da suka fito da kwadayinsu na zama Sanatoci muraran, gwamna Gaidam bai yi zurfi a bukatar son ya zama Sanata ba.

Magoya bayansa na ta kiraye-kiraye gare shi day a fito takarar Sanata, kiran da wasu ke bayyana cewar gwamnan na jin dadinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel