Ga koshi ga kwanan yunwa: Yadda wahalar manoman Najeriya ke tafiya a banza, duba hotuna
Tun bayan zuwan gwamnatin shugaba Buhari ake samun habakar harkokin noma musamman ganin yadda gwamnatin ta rufe iyakokin Najeriya da ake amfani da su wajen shigo da kayan abinci da ragowar wasu kayan masarufi da na amfani yau da kullum.
Sai dai har yanzu manoma basa samun ribar da ya kamata su samu bayan kammala wahalar rainon abinda suka shuka.
Tunda dadewa wasu masana harkar noma da tattalin arziki suka bawa gwamnati shawarar kafa masana’antu domin sarrafa kayan gona da aka samar a gida Najeriya. Masanan sun bayyana cewar hakan ne kadai zai samar da cigaba a bangaren na noma tare da bawa manoma dammar cin ribar guminsu.
Hotunan da ku ke gani a cikin wannna labari, an dauke su ne a kasuwar Tse Kucha dake kusa da masana’antar simintin Dangote dake garin Gboko a jihar Benuwe.
Ana sayar da kwandon Tumatur a kan farashin N150, wasu lokutan ma a kan N100 idan yamma tayi kuma babu masu saya.
A wasu lokutan ma haka manoman ke komawa da kwandunan Tumataransu saboda rashin kasuwa. Manoman haka suke asarar kudin motar zuwa kasuwar da kuma dakon kayan amfanin gonar su.
DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta bukaci yaran Saraki su ajiye mukamansu ko a tsige su
Wannan ba kankanin abin tausayi bane domin akwai kayan amfanin gonad a basa ajiyuwa, irinsu Tumatur da sauransu.
Dole a samu masana’antu a kusa da jama’a da zasu ke sarrafa Tumatur domin saukakawa manoma da kuma habakar arzikinsu da kasa bakidaya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng