Tsintsiya ta watse: Shugabannin kananan hukumomi 13 sun koma PDP a Benue
Akalla shugabannin kananan hukumomi 13 ne a cikin 23 dake a jihar Benue suka canza sheka daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa Peoples Democratic Party PDP biyo bayan komawar gwamnan jihar PDP a satin da ya gabata.
Shugabannin kananan hukumomin dai sun sanar da komar ta su ne PDP a gidan gwamnatin jihar dake a garin Makurdi jim kadan bayan kammala wata tattaunawar sirri da sukayi da Gwamnan a ranar Juma'ar da ta gabata.
KU KARANTA: Rundunar sojin saman Najeriya sun kara yaye matukan jirgin yaki
Legit.ng dai ta samu cewa wadanda suka sauya shekar sun hada da Comfort Echeoda daga karamar hukumar Agatu, Francis Ayaga daga karamar hukumar Gwer ta yamma, Uaah Vitalis daga karamar hukumar Gwer ta gabas, Richard Nyajo daga karamar hukumar Logo, Ibellogo Tor daga karamar hukumar Tyokaa- Ukum, Adakole Abutu daga karamar hukumar Ohimini LGA da kuma Peter Onchedaga karamar hukumar Obi.
Sauran sun hada da Anthony Shawon daga karamar hukumar Guma, Justina Sorka daga karamar hukumar Buruku, Mwuese Ubebe daga karamar hukumar Konshisha, Blessing Unogwo daga karamar hukumar Ado, Virginia Kpindi daga karamar hukumar Katsina-Ala da kuma George Alli daga karamar hukumar Otukpo LGA.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng