Abun kunya: An kama dan Najeriya da hodar iblis mai nauyin 155.5g a kasar Indiya
Sashen yaki da tu’ammali da miyagun kayan maye na jihar Benaluru(NCB) dake kasar Indiya ya sanar da kama wani dan asalin Najeriya, Ozy Chukwudu, da hodar iblis mai nauyin 155.5g a ranar Laraba, 25 ga watan Yuli.
Jami’an NCB sun kama Chukwudu, mai shekaru 30 na haihuwa yayinda suka tsayar da wata mota dake kan hanyar zuwa Bengaluru daga Mumbai.
Rahotanni sun bayyana cewar dama jami’an NCB din na jiran karasowar sa ne bayan samun bayanan sirri a kan muguwar sana’ar safarar miyagun kwayoyi da yake yi.
Tun da farko, wani mutum ne, da ba a bayyana sunansa bay a shigo da hodar iblis din kasar Indiya ta hanyar hadiye ta a wasu kwanso, sannan ya damka tag a Chukwudu domin safarar ta zuwa garin Bengaluru.
A wata takarda da ta raba ga kafafen yada labarai, NCB ta bayyana cewar hodar iblis din zata kai kimanin kudin kasar Indiya Rufi Rs93 a kasuwar kasa da kasa.
DUBA WANNAN: Shugaba Buhari zai bar Najeriya zuwa birnin Lome, duba jerin 'yan rakiyar sa
Yanzu haka dai har an gurfvanar da Chwudu gaban wata kotun kasar Indiya tun ranar Alhamis, 26 ga watan Yuli, 2018.
Kasar Indiya na daga cikin kasashen duniya dake da yawan ‘yan Najeriya. Mafi yawancinsu dalibai ne da kuma masu zuwa domin harkokin kasuwanci.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng