2019: Bangare 3 da fitar Kwankwaso zata yi tasiri a siyasar Kano
A cikin satin da ya kare ne Sanatan jihar Kano ta tsakiya, Rabi’u Musa Kwankwaso, da ragowar wasu mambobin majalisar dattijai da ta wakilai ta jawo barkewar cacar baki da cece-kuce a fadin Najeriya.
Daga cikin wadanda suka canja shekar, labaran fitar Kwankwaso ta fi daukan hankali musamman yadda dumbin magoya bayansa a jihar Kano suka kaure da murnar barin jam’iyyar APC din da ya yi.
Tabbas ficewar Kwankwason daga APC ta girgiza jihar Kano da bikin murna da kona tsintsiya da magoya bayansa suka yi domin nuna sun yi hijira tare da gwaninsu.
Wasu bangare 3 da fitar Kwankwaso zata yi tasiri a kansu a jihar Kano sun hada da;
1. Majalisar dokokin jihar Kano: Damuwar da jama’a da kuma jam’iyyar APC suka nuna a kan yadda fitar Kwankwaso daga APC zata taba majalisar dokokin jihar Kano ne ya saka shugaban majalisar, Alhaji Yusuf Atta, fitowa ya bayyana cewar har yanzu suna tare da APC.
Atta ya bayyana cewar daga cikin mambobin majalisar dokokin 40, 33 na biyayya ne ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Saidai duk da wannan bayani na Atta, masu nazarin siyasar Kano da kuma irin yadda tafiyar Kwankwasiyya keda magoya baya a lunguna da sakon jihar, sun tabbatar da cewar zaben 2019 zai kawo sabbin fuska da zasu ci zaben majalisar albarkacin Kwankwaso.
2. Zaben Shugaban kasa: Da adadin mutane miliyan fiye da miliyan 4 da suka yi rijistar zabe a Kano, jihar zata taka muhimmiyar rawa a zaben shugaban kasa na 2019.
Duk da har yanzu shugaba Buhari na da magoya baya a Kano da arewacin Najeriya, a bayyane take cewar kuri’unsa zasu ragu saboda ficewar Kwankwaso.
DUBA WANNAN: An kulla sharudan yin aiki tare tsakanin Shekarau da Kwankwaso a PDP
3. Siyasar Kwankwaso: Saidai duka da yawan magoya baya da yake da su a Kano, wasu na ganin cewar 2019 zata zama manuniya ga akidar Kwankwasiya.
Ya zuwa yanzu dai babu tabbacin ko Kwankwaso zai nemi takarar shugabancin kasa a PDP da karfinsa. Kazalika babu tabbacin ko jam’iyyar zata gan shi da mutunci kamar yadda yake da shi a jam’iyyar a baya.
Mai yiwuwa tasirin Kwankwaso a siyasar Kano da ma kasa baki daya ya zo a karshe a 2019 matukar bai iya kafa gwamnati a jihar Kano ba, wato idan gwamna Ganduje ya zarce.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng