Kasurgumin dan daban da ya kware wajen kisa, fashi da ta'ddanci ya shiga hannu a Kano
Rahotanni sun kawo cewa gasurgumin dan daban da ya kware wajen kisa, fashi da ta'ddanci ya shiga hannu a jihar Kano.
An kama dan fashin mai suna Hafizu Magaji a yankinsu na Tudun Murtala bayan ya addabi mutanen Tudun Murtala, Rimin Kebe, Kwana Hudu da wasu sassan unguwanni na birnin Kano kamar su Bakin Kasuwa, Bakin Zuwo da Jakara.
Ya shahara wajen sata, kwace har da kisan kai a lokaci daba-daban.
KU KARANTA KUMA: Taimakon Turawan Yamma: Mutum 10m a Najeriya zasu mori data kyauta har abada a birane da dama a badi
Ya fada tarkon jami’an 'yan sandan Kano ne lokacin da ya yi arangama da 'yan banga da misalin karfe biyun dare yana kokarin fasa wani shago kuma kafin kama shi sai da ya sassari 'yan bangan akalla guda uku kafin a kai ga nasarar cafke shi.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha yayi alkawarin bayar da naira miliyan 20 ga duk mutumin da ya bayar da bayani mai amfani akan wadanda suka kashe jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar.
Gwamnan ya dauki wannan alkawari ne a ranar Juma’a, sa’o’i kadan bayan wasu yan bindiga sun kashe shugaban APC a karamar hukumar Ideato ta arewa, Mista Sunny Ejiagwu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng