Buhari zai bude hanyoyin ruwan da ke Kogi da Neja – Shugaban NIWA

Buhari zai bude hanyoyin ruwan da ke Kogi da Neja – Shugaban NIWA

Shugaban Hukumar hanyoyin ruwa na kasar nan Danladi Ibrahim ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta kammala aiki a tashar ruwa na Baro da ke cikin Jihar Neja kuma za a fara aiki nan ba da dadewa ba.

Babban Darektan na NIWA ya bayyanawa ‘Yan jarida cewa an kammala aikin tashar ruwa da ke Baro da kuma babbar tashar da ke garin Lokoja a cikin Jihar Kogi. Yanzu Shugaba Buhari kurum ake jira ya sa hannu a bude tashoshin.

Danladi Ibrahim ya tabbatar da cewa kafin shekarar nan ta kare za a soma aiki a tashoshin ruwan. An kuma ware kudi a kasafin shekarar nan domin gina titi daga Baro zuwa Garin Lokoja har zuwa babban Birnin Tarayya na Abuja.

KU KARANTA: Sanatocin APC kusan 10 sun yi watsi da gayyatar Shugaba Buhari

Bayan wannan kuma akwai wasu tashoshin ruwa da ke Jihar Imo da Anamra a Kudancin Kasar. Ana sa rai ba tare da bata lokaci ba za a gama aikin tashar Oguta da na Onitsha inji Shugaban NIWA na kasar da ke rikon kwarya.

Ana kuma shirin kammala yasar ruwan Benuwai da na Neja kafin 2019. Wannan dai zai taimaka waje samawa dinbin jama’a aikin yi a Kasar. Daukar kaya daga Legas da Kudancin kasar zuwa Arewa zai zama cikin sauki nan gaba.

Kafin wa’adin wannan Gwamnati ya cika ake so a yashe manyan ruwan da ke kasar domin a sawake jigila. An dai dauki shekara da shekaru ana jira Gwamnati ta tada tashar baro da ke Neja ba a samu ba sai zuwan Gwamnatin nan.

A makon nan kun ji cewa wani babban ‘Dan kasuwa a Katsina zai gina matatar mai a Garin Mashi da ke Jihar. Gwamnatin Buhari ce tayi sanadiyyar samawa mutane aikin yi ta harkar man fetur

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel