Komawar Shekarau APC: Bayanai na baya-bayan nan daga bangarensa
- An dauka Shekarau na iya komawa APC
- Sule Ya'u Sule ya karyata zancen daga Daily Trust
- A yanzu Malam din yana PDP ne tare da Kwankwaso
Mai magana da yawun Malam Ibrahim Shekarau, Sule Yau Sule, a hirarsa da majiyarmu, ya karyata zancen cewa wai ana tattaunawar sirri tsakanin jam'iyyar APC da Malam Shekarau, mai takarar shugaban kasa a PDP.
A cewarsa, babu wannan batun, domin kuwa, MAlamin yana nan daram a PDP kuma babu wani kishin-kishin ya zuwa yanzu a karkashin kasa.
An so dai ace wai Malam din, ya koma APC ya bada Malam Salisu Sagir Takai a matsayin mataimakin gwamna don a kada PDP a jihar.
DUBA WANNAN: Wata duniyar zata matso kusa da tamu
Zaman Malam Kwankwaso da Malam Shekarau dai a wuri daya ba ga nan ba, duba da cewa a shekaru 15 na siyasar Kano, wasu har rasa ransu suka yi don shuwagabannin nasu su kai gaci. Ko Malam din zasu jitu da Kwankwaso a PDP? Wannan shine abin tambaya.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng