Kasassabar wani jami’in Dansanda ta ja masa bayan ya dirka ma wani matashi harsashi
Hankula sun tashi a garin Beji na jihar Neja bayan da wani jami’in Dansanda ya daddage ya dirka ma wani matashi mai shekaru goma sha takwas harsashi sakamakon kacamewar rikici tsakanin matasan garin da Yansanda.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Alhamis, 26 ga watan Yuli yayin da jami’an Yansanda suka isa kasuwar garin inda aka kama wani mutumi da zargin yayi amfani da tsafi wajen sace ma wani mutumi mazakutarsa, wanda hakan ya sanya matasan yankin lakada masa duka suna neman kashe shi.
KU KARANTA: Hatsari ba sai a Mota ba: Mutane 5 sun gamu da ajalinsu yayin da Kwalekwale ta kifa dasu
Isar Yansanda ke da wuya, sai suka kwato mutumin, inda suka jefa cikin motarsu tare da hadin kan wasu yan banga dake aiki a yankin, bayan haka ne sai wani Dansanda yayi kokarin korar mutane daga inda suke ta hanyar harbin iska da bindigarsa, a haka ne harbin ya samu wani matashi, kuma ya mutu nan take.
Wannan lamari yayi matukar harzuka matasan, inda sama da matasa dari bakwai suka tare hanyar Beji zuwa Zungeru, tare da kai ma Yansandan da yan bangar hari da duwatsu, kamar yadda Kaakakin rundunar Yansandan jihar,DSP Mohammed Abubakar ya bayyana.
Daga karshe DSP yace sun kaddamar da bincike akan lamarin, sa’annan an mika gawar mamain zuwa dakin ajiyan gawarwaki, yayin da shima mutumin da ake zargin an sace masa mazakuta an garzaya da shi Asibiti don jin gaskiyar zargin, yayin da wanda ake zargi da tsafin yake hannun Yansanda don amsa tambayoyi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng