Koma baya: Baitul-malin Najeriya na ta yin kasa a wata 3 a jere
Rahotannin da muke samu daga babban bankin Najeriya yana nuni ne da cewa baitul-malin kasar Najeriya na ta cigaba da raurayewa a watanni uku da suka shude a jere kamar dai yadda alkalumman da suka fitar jiya suka nuna.
Rahoton da babban bankin ya fitar dai a ranar Larabar da ta gabata ya nuna cewa baitul-malin yanzu haka dalar Amurka biliyan 47.303 wanda yake nuna cewa dalar Amurka miliyan 394 ce ta zurare a kwanaki 13 kacal da suka gabata.
KU KARANTA: Canza sheka: Shekarau ya gindayawa Kwankwaso sharuddan zaman lafiya
A wani labarin kuma, Jami'an hukumar nan dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC a Najeriya ranar Alhamis sun gurfanar da wani mutum mai suna John Abebe dake zaman suruki ga tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo a kotu.
Mista John Abebe wanda kani ne ga marigayiya tsohuwar matar Cif Obasanjo, Stella Obasanjo din EFCC ta ce ta gurfanar da shi ne a kotun bisa zargin sa da suke yi da anfani da takardun bogi wajen neman aikin hakar mai daga Najeriya din.
Asali: Legit.ng